2 Tarihi 17:1-18 HAUCB2020 - Bible AI

1Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki ya kuma kahu sosai gāba da Isra’ila.

2Ya kafa mayaƙa a dukan biranen katangar Yahuda, ya kuma sa runduna a Yahuda da kuma a garuruwan Efraim da mahaifinsa Asa ya ci da yaƙi.

3Ubangiji* kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba

4amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi.

5Ubangiji* ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma.

6Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji*, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda.

7A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda.

8Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram.

9Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji* tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane.

10Tsoron Ubangiji* ya kama dukan masarautun ƙasashen da suke kewaye da Yahuda, har ba su yi yaƙi da Yehoshafat ba.

11Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.

12Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda

13da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima.

14Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka.

15biye da shi, Yehohanan shi ne shugaba, yana da sojoji 280,000;

16biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji*, yana da sojoji 200,000.

17Daga Benyamin,

18biye da shi, Yehozabad, yana da sojoji 18,000 shiryayyu don yaƙi.

le>