1Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok.
2Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji*, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji* kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci.
3Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji*, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel.
4Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi.
5Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku.
6Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji* Allahnsa.
7Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.
8Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida.