Amos 7:1-16 HAUCB2020 - Bible AI

1Ga abin da Ubangiji* Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji* yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa.

2Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji* Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”

3Saboda haka sai Ubangiji* ya dakatar da nufinsa.

4Ga abin da Ubangiji* Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji* Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa.

5Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji* Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”

6Saboda haka sai Ubangiji* ya dakatar da nufinsa.

7Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.

8Sai Ubangiji* ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?”

9“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku

10Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba.

11Gama ga abin da Amos yake cewa,

12Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can.

13Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”

14Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.

15Amma Ubangiji* ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’

16Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji*. Ka ce,

Hausa Contemporary Bible™ © 2020 by Biblica, Inc.® Used by permission. All rights reserved worldwide.
div>