Ezekiyel 18:1-31 HAUCB2020 - Bible AI

1Maganar Ubangiji* ta zo mini cewa,

2“Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,

3“Muddin ina raye, in ji Ubangiji* Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.

4Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.

5“A ce akwai mai adalci

6ba ya cin abinci a duwatsun tsafi

7Ba ya cin zalin wani,

8Ba ya ba da bashi da ruwa

9Yana bin ƙa’idodina

10“A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa+ 18:10 Ko kuwa abubuwa ga ɗan’uwa*

11(ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).

12Yakan ci zalin matalauta da mabukata.

13Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.

14“Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,

15“Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba

16Bai ci zalin wani

17Yakan janye hannunsa daga zunubi+ 18:17 Seftuwajin (duba kuma aya 8); Ibraniyanci daga matalauta*

18Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.

19“Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu.

20Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.

21“Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

22Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu.

23Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji* Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?

24“Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.

25“Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce?

26In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.

27Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa.

28Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

29Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?

30“Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji* Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba.

31Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?

le>