1Ubangiji* ya ce wa Musa,
2“Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.
3Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji*, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.
4Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji*.
5“Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi.
6A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji*.
7Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji*.
8Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji* kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.
9Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji*.”
10To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani.
11Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji*, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.)
12Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji* ya nuna musu abin da za su yi da shi.
13Sai Ubangiji* ya ce wa Musa,
14“Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu.
15Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa,
16duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji*, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji*, dole a kashe shi.
17“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
18Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
19Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi;
20karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
21Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
22Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji* Allahnku.’ ”