1To, fa, sai Ubangiji* ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.
2Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.”
3(Ubangiji* ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)
4Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji* ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar.
5Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu.
6Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba.
7Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji* zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.
8Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.
9Ubangiji* ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.”