Fitowa 15:1-26 HAUCB2020 - Bible AI

1Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji* suka ce,

2“Ubangiji* ne ƙarfina da mafakata,

3Ubangiji* mai yaƙi ne

4Karusan Fir’auna da sojojinsa

5Zurfafan ruwaye sun rufe su;

6Hannun damanka, ya Ubangiji*,

7“A cikin girman kwarjininka

8Da hucin numfashin hancinka

9Magabci ya yi fahariya, cewa

10Amma ka hura numfashinka

11Wane ne cikin alloli,

12“Ka miƙa hannunka na dama,

13A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe

14Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki

15Sarakunan Edom za su tsorata,

16Razana da tsoro za su fāɗo a kansu.

17Za ka kawo su, ka dasa su

18“Ubangiji* zai yi mulki

19Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji* ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

20Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.

21Miriyam ta yi musu waƙa.

22Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.

23Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).

24Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”

25Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji*, Ubangiji* kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi.

26Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji* Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji* da nake warkar da ku.”

>