1Sa’an nan Ubangiji* ya ce wa Musa,
2“Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.
3Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
4Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.
5Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
6“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
7ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.
8Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
9“Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.
10Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
11Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
12“Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.
13Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.
14Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.
15Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”
16Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji* ya umarce shi.
17Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.
18Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.
19Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
20Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.
21Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
22Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.
23Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji*, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
24Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul
25ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji*, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
26Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen
27ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
28Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.
29Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji* ya umarce shi.
30Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,
31a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.
32Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji* ya umarci Musa.
33Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
34Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji* ta cika tabanakul.
35Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji* kuwa ta cika tabanakul.
36Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.
37Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.
38Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.