Hosiya 1:1-10 HAUCB2020 - Bible AI

1Maganar Ubangiji* da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash+ 1:1 Da Ibraniyanci Yowash, wani suna na Yehowash* sarkin Isra’ila.

2Sa’ad da Ubangiji* ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji* ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji*.”

3Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.

4Sai Ubangiji* ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.

5A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”

6Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji* ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama,+ 1:6 Lo-Ruhama yana nufin ba tausayi.* gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu.

7Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji* Allahnsu.”

8Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji.

9Sai Ubangiji* ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi,+ 1:9 Lo-Ammi yana nufin ba mutanena ba.* gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.

10“Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’