Hosiya 3:1-4 HAUCB2020 - Bible AI

1Ubangiji* ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji* yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”

2Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir.

3Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare+ 3:3 Ko kuwa jira* da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare+ 3:3 Ko kuwa jira* da ke.”

4Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki.

Hausa Contemporary Bible™ © 2020 by Biblica, Inc.® Used by permission. All rights reserved worldwide.
/div>