Irmiya 1:1-18 HAUCB2020 - Bible AI

1Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin.

2Maganar Ubangiji* ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda,

3da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta.

4Maganar Ubangiji* ta zo mini cewa,

5“Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san+ 1:5 Ko kuwa zaɓe* ka,

6Sai na ce, “Kayya, Ubangiji* Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.”

7Amma Ubangiji* ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka.

8Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji*.

9Sai Ubangiji* ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka.

10Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.”

11Maganar Ubangiji* ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?”

12Ubangiji* ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.”

13Maganar Ubangiji* ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?”

14Ubangiji* ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar.

15Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji*.

16Zan furta hukunci a kan mutanena

17“Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu.

18Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta.