Irmiya 45:1-4 HAUCB2020 - Bible AI

1Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,

2“Ga abin da Ubangiji*, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.

3Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji* ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”

4Ubangiji* ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji* yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.