Ishaya 20:1-5 HAUCB2020 - Bible AI

1A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi,

2a wannan lokaci Ubangiji* ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

3Sa’an nan Ubangiji* ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,+ 20:3 Wato, yankin Nilu na Bisa; haka ma a aya 5*

4haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.

5Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.