Ishaya 39:1-7 HAUCB2020 - Bible AI

1A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa.

2Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba.

3Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?”

4Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?”

5Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji* Maɗaukaki.

6Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji*.

7Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”