Ishaya 4:1-5 HAUCB2020 - Bible AI

1A wannan rana mata guda bakwai

2A wannan rana Reshen Ubangiji* zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.

3Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima.

4Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.

5Sa’an nan Ubangiji* zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.

Hausa Contemporary Bible™ © 2020 by Biblica, Inc.® Used by permission. All rights reserved worldwide.
/div>