Karin Magana 3:1-34 HAUCB2020 - Bible AI

1Ɗana, kada ka manta da koyarwata,

2gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa

3Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai;

4Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau

5Ka dogara ga Ubangiji* da dukan zuciyarka

6cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

7Kada ka zama mai hikima a ganinka;

8Wannan zai ba wa jikinka lafiya

9Ka girmama Ubangiji* da dukan dukiyarka,

10ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,

11Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji*

12domin Ubangiji* yakan hori waɗanda yake ƙauna,

13Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,

14gama ta fi azurfa riba

15Ta fi lu’ulu’u daraja;

16Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;

17Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,

18Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;

19Ta wurin hikima Ubangiji* ya kafa harsashin duniya,

20ta wurin sani aka rarraba zurfafa,

21Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,

22za su zama rai a gare ka,

23Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,

24sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

25Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya

26gama Ubangiji* zai zama ƙarfin halinka

27Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace,

28Kada ka ce wa maƙwabcinka

29Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka,

30Kada ka zargi mutum ba dalili,

31Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye

32Gama Ubangiji* yana ƙyama mai aikata mugunta

33La’anar Ubangiji* tana a gidan mugaye,

34Yakan yi wa masu girman kai ba’a

ticle>