Maimaitawar Shari’a 10:1-21 HAUCB2020 - Bible AI

1A lokacin Ubangiji* ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.+ 10:1 Wato, akwatin alkawari*

2Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”

3Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana.

4Ubangiji* kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji* ya ba ni su.

5Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji* ya umarce ni, kuma suna can a yanzu.

6(Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist.

7Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

8A lokacin Ubangiji* ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji*, su tsaya a gaban Ubangiji*, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.

9Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji* ne gādonsu yadda Ubangiji* Allahnku ya faɗa musu.)

10To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji* kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku.

11Ubangiji* ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”

12Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji* Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji* Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji* Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

13ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji* da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

14Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji* Allahnku ne.

15Duk da haka Ubangiji* ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau.

16Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17Gama Ubangiji* Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.

18Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.

19Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.

20Ku ji tsoron Ubangiji* Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.

21Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.

ter>