1Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji* Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka,
2saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji* Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.
3Ku ji, ya Isra’ila, ku kuma kula, ku kiyaye su don yă zama muku da lafiya, ku kuma ƙaru sosai a ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji*, Allahn kakanninku ya yi muku alkawari.
4Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji* Allahnmu, Ubangiji* ɗaya ne.
5Ku ƙaunaci Ubangiji* Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.
6Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.
7Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
8Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.
9Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
10Sa’ad da Ubangiji* Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba,
11gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi,
12ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji* wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba.
13Ku ji tsoron Ubangiji* Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa.
14Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku;
15gama Ubangiji* Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.
16Kada ku gwada Ubangiji* Allahnku kamar yadda kuka yi a Massa.
17Ku tabbata kun kiyaye umarnan Ubangiji* Allahnku, da farillansa da kuma ƙa’idodinsa da ya ba ku.
18Ku aikata abin da yake daidai da kuma mai kyau a idon Ubangiji*, don yă zama muka da lafiya, ku kuwa shiga ku mallaki ƙasa mai kyau da Ubangiji* ya yi alkawari da rantsuwa ga kakanninku.
19Zai kuwa korin dukan abokan gābanku da suke gabanku, yadda Ubangiji* ya faɗa.
20Nan gaba, sa’ad da ’ya’yanku suka tambaye ku, “Mene ne ma’anar farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji* Allahnmu ya umarce ku?”
21Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji* ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi.
22A idanunmu Ubangiji* ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa.
23Amma ya fitar da mu daga can domin yă kawo mu cikin ƙasar da ya yi wa kakanninmu alkawari tare da rantsuwa zai ba mu.
24Ubangiji* ya umarce mu mu yi biyayya da dukan waɗannan ƙa’idodi, mu kuma ji tsoron Ubangiji* Allahnmu, saboda kullum mu ci gaba, a kuma bar mu da rai, kamar yadda yake a yau.