Mattiyu 5:1-47 HAUCB2020 - Bible AI

1Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna.

2sai ya fara koya musu.

3“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,*

4Masu albarka ne waɗanda suke makoki,*

5Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,*

6Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,*

7Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,*

8Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,*

9Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,*

10Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,*

11“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.*

12Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.*

13“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.*

14“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.*

15Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.*

16Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.*

17“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.*

18Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.*

19Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.*

20Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.*

21“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;*+ 5:21 Fit 20.13*kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’*

22Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘+tl Raka+tl*,’*+ 5:22 Kalmar Arameyik ta reni*za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.*

23“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,*

24sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.*

25“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.*

26Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.*

27“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’*+ 5:27 Fit 20.14*

28Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.*

29In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.*

30In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.*

31“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’*+ 5:31 M Sh 24.1*

32Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.*

33“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’*

34Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;*

35ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.*

36Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.*

37Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.*

38“Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’*+ 5:38 Fit 21.24; Fir 24.20; M Sh 19.21*

39Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.*

40In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.*

41In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.*

42Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.*

43“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka,*+ 5:43 Fir 19.18*ka kuma ƙi abokin gābanka.’*

44Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku*+ 5:44 Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke la’antarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri*kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,*

45don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.*

46In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?*

47In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?*

>