1“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta,*
2Ka farka! Ka ƙarfafa abin da ya rage wanda kuma yake bakin mutuwa, don ban ga ayyukanka cikakke ne ba a gaban Allahna.*
3Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba.*
4Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta.*
5Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.*
6Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.*
7“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta,*
8Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba.*
9Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka.*
10Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.*
11Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.*
12Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana.*
13Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.*
14“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta,*
15Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi!*
16Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.*
17Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.*
18Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.*
19Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.*
20Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.*
21Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.*