1Ya Allah, wanda nake yabo,
2gama mugaye da masu ruɗu
3Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni;
4A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi,
5Sun sāka mini alheri da mugunta,
6Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi;
7Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi,
8Bari kwanakinsa su zama kaɗan;
9Bari ’ya’yansa su zama marayu
10Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara;
11Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi;
12Bari kada kowa yă yi masa alheri
13Bari duk zuriyarsa su mutu,
14Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji*;
15Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji* kullum,
16Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba,
17Yana jin daɗin la’antarwa,
18Ya sa la’antarwa kamar rigarsa;
19Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi,
20Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji* ga masu zargina,
21Amma kai, ya Ubangiji* Mai Iko Duka,
22Gama ni matalauci ne mai bukata kuma,
23Na ɓace kamar inuwar yamma;
24Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi;
25Na zama abin dariya ga masu zargina;
26Ka taimake ni, ya Ubangiji* Allahna;
27Bari su san cewa hannunka ne,
28Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka;
29Masu zargina za su sha kunya
30Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji* sosai;