1Yabi Ubangiji*.+ 113:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9.*
2Bari a yabi sunan Ubangiji*,
3Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,
4Ana ɗaukaka Ubangiji* a bisa dukan al’ummai,
5Wane ne yake kamar Ubangiji* Allahnmu,
6wanda yake sunkuya yă dubi
7Yakan tā da matalauta daga ƙura
8ya zaunar da su tare da sarakuna,