1Ku gode wa Ubangiji*, gama nagari ne shi;
2Bari Isra’ila yă ce,
3Bari gidan Haruna yă ce,
4Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji* su ce,
5Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji*,
6Ubangiji* yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
7Ubangiji* yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
8Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji*
9Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji*
10Dukan al’ummai sun kewaye ni,
11Sun kewaye ni a kowane gefe,
12Sun rufe ni kamar ƙudan zuma,
13An ture ni baya na kusa fāɗuwa,
14Ubangiji* ne ƙarfina da waƙata;
15Sowa ta farin ciki da nasara
16An ɗaga hannun dama na Ubangiji* sama;
17Ba zan mutu ba amma zan rayu,
18Ubangiji* ya hore ni sosai,
19Buɗe mini ƙofofin adalci;
20Wannan ne ƙofar Ubangiji*
21Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini;
22Zabura Dutsen da magina suka ƙi
23Ubangiji* ne ya yi haka,
24Wannan ita ce ranar da Ubangiji* ya yi;
25Ya Ubangiji*, ka cece mu;
26Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji*.
27Ubangiji* shi ne Allah
28Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;