Zabura 134:1-3 HAUCB2020 - Bible AI

1Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.

2Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji.

3Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.

>