Zabura 3:1-8 HAUCB2020 - Bible AI

1Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!

2Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela+ 3:2 Kalmar da ba a tabbatar da ma’anarta ba, mai bayyana sau da sau a cikin Zabura; mai yiwuwa kalma ce ta kiɗi.

3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.

8Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Hausa Contemporary Bible™ © 2009, 2020 by Biblica, Inc.® Licensed under CC BY-SA 4.0 where published as Open Hausa / open.bible.
/div>