1Zan gode wa Ubangiji* kullayaumi;
2Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji*;
3Ku ɗaukaka Ubangiji* tare da ni;
4Na nemi Ubangiji*, ya kuwa amsa mini;
5Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;
6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji* kuwa ya ji shi;
7Mala’ikan Ubangiji* ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
8Ku gwada ku gani cewa Ubangiji* yana da kyau;
9Ku ji tsoron Ubangiji*, ku tsarkakansa,
10Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
11Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
12Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
13ka kiyaye harshenka daga mugunta
14Juyo daga mugunta ku yi alheri;
15Idanun Ubangiji* suna a kan masu adalci
16fuskar Ubangiji* yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta,
17Adalai kan yi kuka, Ubangiji* kuwa yakan ji su;
18Ubangiji* yana kusa da waɗanda suka karai
19Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
20yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
21Mugunta zai kashe mugu;