1Ya Ubangiji*, Allahn da yake ramuwa,
2Ka tashi, ya Alƙalin duniya;
3Har yaushe mugaye, ya Ubangiji*
4Suna ta yin maganganun fariya;
5Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji*;
6Suna kashe gwauraye da kuma baƙi;
7Suna ce, “Ubangiji* ba ya gani;
8Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;
9Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne?
10Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne?
11Ubangiji* ya san tunanin mutum;
12Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji*,
13kana ba shi sauƙi a lokacin wahala,
14Gama Ubangiji* ba zai ƙi mutanensa ba;
15Za a sāke kafa hukunci a kan adalci,
16Wane ne zai yi gāba da mugaye domina?
17Da ba don Ubangiji* ya yi mini taimako ba,
18Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”
19Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
20Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,
21Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci
22Amma Ubangiji* ya zama kagarata,