1A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji* ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.
2Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji*
3ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji* Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?”
4Sai maganar Ubangiji* Maɗaukaki ta zo mini ta ce,
5“Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?
6Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba?
7Ashe, ba kalmomin da Ubangiji* ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ”
8Sai maganar Ubangiji* ta sāke zuwa wa Zakariya cewa,
9“Ga abin da Ubangiji* Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.
10Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
11“Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.
12Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji* Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji* Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.
13“ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji* Maɗaukaki.